Connect with us

Labarai

An Samu Mutuwar Aure 999 A Kasa Da Shekara Daya a Jihar Kano – Rahoton IHRC

Published

on

Daga: Nura Ahmad Hassan

Wani rahoto da wata kungiya mai fafutukar kare haqqin bil’adama wato International Human Right Commission (IHRC), ta fitar ta koka kan yadda aka samu karuwar mace macen aure a jihar Kano, a daga shekarar 2022 zuwa 2023.

Kungiyar ta (IHRC) reshen Kano, cikin sanarwar mai dauke da sa hannun Babban jami’inta Kwamared Hafiz Sunusi Sanka, ta ce akwai matukar damuwa kan yadda mutuwar aure da sauran matsalolin da suka shafi aure suka yi mummunar yawaita.

”Mun fitar da wannan takarda ne domin jawo hankalin masu ruwa da tsaki kan sha’anin al’ummah da zamantakewarsu  a fadin jihar Kano, bisa la’akari da kididdigar dake hannun mu kan yadda ake samun ƙaruwar mutuwar aure a jihar nan cikin kankanin lokaci, domin daukar matakan gaggawa.”

”Korafe Korafen da suka shafi auratayya da ma’aurata da Kungiyar mu ta samu kuma tayi aiki akai, sun kai 288 a  shekarar 2022, amma a 2023 da muke ciki matsalar tayi tashin gwauron zabbi, kawo yanzu, kungiya ta karbi Korafe korafe daga ma’aurata da ya kai 1080, kusan ninki 4 kenan na abinda aka samu a 2022.

Cikin wannan adadi na 1080, aure 999 ne ya mutu, wato sama da kashi 90 cikin dari na adadin korafin da kungiya ta samu, yayin da aure 50 ke  gaban kuliya a kotuna daban daban.

Mun fahimci cewa yawan mutuwar aure barkatai na jefa rayuwar yara wadanda sune manyan gobe cikin mummunan hali, yakamata a lalubo hanyar dakatar da yawan mutuwar auren, kafin abubuwa su kara lalacewa.

Wasu daga cikin dalilan da muke ganin na jawo mutuwar auren a yanzu, kamar yadda binciken mu ya nuna, sun hadar da:

1. Talauci
2. Karancin ilmin zamantakewa
3. Rashin tsari a rayuwa
4. Iyaye/Abokai/ƙawaye

*AUREN ZAURAWA*
A wannan gabar, duba da bayanan da suka gabata a sama, kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya reshen jihar Kano na kallon yunkurin gwamnati na aurar da zaurawa kyauta, a matsayin wani tallafi da zai taimaka wajen cigaban al’ummarmu.

Kuma idan anyi shi yanda yakamata shirin zai taimaka wajen rage badala, da ayyukan ta’addanci a tsakanin al’ummah.

A matsayin mu na daya daga cikin masu ruwa da tsaki a jihar Kano, kungiya na baiwa gwamnatin Kano wadannan shawarwari domin samun dorewar nasarar shirin.

Na farko – duk angon/amaryar da yake/take  da shedar karatu da a daukesu aikin gwamnati na  din-din-din,ko a taimaka musu akan sana’o’insu.

Na biyu – gabatar da taron bita domin wayar da kan ma’auratan kan rayuwar auren akai-akai, ta hanyar dauko malaman addinin musulunci da na zamani da masana halayyar dan’adam.

Na uku – Kafa wani kwamiti na musamman da zai dinga bibiyar yadda zaman auren ke kasancewa, domin tarar matsala tare da warware ta tun tana ƙarama.

Daga karshe muna fatan dukkan wadannan matakai da shawarwari zasu taimaka wajen raguwar mutuwar aure a jihar Kano.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa Qungiyar Kare haqqin bil’adama ta duniya(INTERNATIONAL HUMAN RIGHT COMMISSION) reshen jihar Kano ta karkare da bayyana fatan ta na ganin jihar Kano ta cigaba da bunkasa.

Advertisements
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *